PDP: Fitar Atiku ba za ta canza komai ba

Ahmed Gulak Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ahmed Gulak, mai baiwa Shugaban Nijeriya shawara kan harkokin siyasa

A Najeriya, bangaren shugaban kasar ya ce bai yi mamakin sauya-shekar da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar adawa ta APC ba.

Bangaren shugaban kasar ya yi zargin cewa tun lokacin da Atiku Abubakar ya sake komawa a jam'iyyar ta PDP, bai saki jikinsa a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar ba.

Barrister Ahmed Gulak mai baiwa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin siyasa, ya bayyana cewar ba zai rage ma jam'iyyar PDP ba komai ba.

Ahmed Gulak yace, yayinda wasu ke fita daga PDP suna komawa APC, wasu 'yan APC din na fita suna komawa PDP.

Karin bayani