Obj da Buhari sun kauracewa taro da Jonathan

Image caption Wasu daga cikin tsaffin Nigeria sun halarci taron

Tsofoffin shugabannin Nigeria, Cif Olusegun Obasanjo da Janar Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi duk sun kauracewa taron majalisar kasa da ake yi a fadar shugaban kasar dake Aso rock.

Taron majalisar kasar wacce ta kunshi tsaffin shugabannin kasar da tsaffin manyan joji da gwamnonin jihohin kasar da shugaban majalisar wakilai da na dattijjai anayinsa ne karkashin jagorancin Shugaba Goodluck Jonathan.

Sai dai kuma tsaffin shugabannin kasar, Yakubu Gowon da Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalam Abubakar da kuma Earnest Shonekan duk sun halarcin taron.

Ana saran taron zai mayar da hankali a kan batutuwan tsaro da kuma makomar siyasar kasar.

A irin wannan taron da aka yi a Maris ne, majalisar kasa ta amince da yi wa tsohon gwamnan jihar Bayelsa afuwa.