Sanusi ya zargi NNPC kan kudin man fetur

Hakkin mallakar hoto getty and reuters
Image caption Sanusi ya ce NNPC ya sayar da danyen mai na $67bn amma ya aikewa Babban Bankin $47 bn.

Shugaban Babban Bankin Nigeria, Sanusi Lamido Sanusi, ya ce kamfanin man fetur na kasar, NNPC bai shigar da $20bn na man da ya sayar a cikin asusun babban bankin ba.

Mallam Sanusi ya bayyana haka ne yayin da ya halarci zaman jin bahasin jama'a da kwamitin harkokin kudi na majalisar dattawan kasar ya gudanar ranar Talata.

Ya ce NNPC ya sayar da danyen mai na $67bn amma ya aikewa Babban Bankin $47 bn.

Malam Sanusi ya ce akwai bukatar NNPC ya sanar da duniya inda $20bn suke.

A kwanakin baya ne dai rikici ya kaure tsakanin Malam Sanusi da shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan.

Hakan ya faru ne bayan shugaban kasar ya yi zargin cewa Sanusi ne ya tsegunta wasikar da ya rubuta masa inda ya yi ikirarin cewa NNPC bai bayyana yadda ya yi da dala biliyan 49.8 na kudaden danyen man da ya sayar ba.

Karin bayani