Ana kokarin janyo bore a Saudi Arabia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Shugaban jami'an tsaro na Askar a Saudi Arabia ya ce suna kokarin murkushe ayyukan masu tsatsauran ra'ayi a tsakanin jami'ansu.

An ambato Sheikh Abdel Latif al-Sheikh a wata jaridar Saudiyya yana cewar masu tsatsauran ra'ayin na kokarin janyo bore a cikin kasar.

Kalamansa na zuwa ne bayan wata doka da aka kafa a ranar Litinin wacce ta gindaya daurin shekaru kusan 20 ga duk 'yan Saudiyyan da suka shiga yaki a cikin wata kasa ko kuma suka shiga cikin wata kungiya ta 'yan ta'adda.

Matasan Saudiyya da dama ne suka tsallaka zuwa Syria don yaki a bangaren dakarun 'yan tawaye masu kishin Islama.

Karin bayani