Gargadi kan wata mummunar cutar sankara

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO
Image caption Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadi game da wata mummunar cutar kansa ko sankara dake lakume rayukkan mutane a duniya.

Hukumar tace, za a iya kare mutane daga kamuwa da cutar ta kansa, tace ana bukatar a kara maida kai ga maganin kiba da shaye-shayen giya da taba.

WHO din tace ana gaya ma mutane miliyan goma sha-4 kowacce shekara cewar suna da cutar kansa, to amma ana hasashen adadin zai karu zuwa miliyan 24 cikin shekaru ashirin masu zuwa.

Hukumar lafiyar ta duniya ta yi gargadin cewa kudin maganin cutar na karuwa fiye da kima.

Tace ya kamata gwamnatoci su dauki tsauraran matakai na hana shan barasa da shan sukari ta hanyar kara farashin su da takaita tallace-tallacen su.