An dasawa dan Denmark Hannun Roba

Hannun Robar da aka kera Hakkin mallakar hoto Lifehand
Image caption An dai dasawa Mr Aabo hannun ne bayan da ya rasa hannunsa a wani hadarin wuta a lokaciun da yake wasa da ita.

Wanda aka yankewa hannu dan kasar Denmark ya zama mutum na farko da aka dasa masa hannun roba wanda zai ba da damar jin wani abu daga 'yan yatsun da aka kera na na'ura.

Masu aikin tiyatar a kasar Italiya sun jona hannun da jijiyoyin a allon kafadar Dennis Aabo wanda zai ba shi damar amfani da nannun tamkar na gaske da kwakwalwarsa ke sarrafawa.

Mr Aabo wanda ya rasa hannunsa a lokacin da yake wasan wuta da ake kira Fire Works a turance yace ya samu damar jin abuy da kuma taurinsa da ma siffarsa ba tare da ya kalle shi ba.

Mr Aabo yace ya na jin dadin sakwannin da ke danganawa ga jijiyoyi daga kwakwalwa domin kuwa zai iya jin cewa ya na rike da wani abu, da kuma yadda 'yan yatsun ke cafkar abu sai ya ji tamkar na gaske ne.

Karin bayani