Cece-kuce kan kasafin kudin Najeriya

Majalisar Najeriya Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption An dade ana ta cece-kuce tsakanin 'yan majalisar da suka fito daga jam'iyyar PDP da kuma takwarorinsu na jam'iyyar adawa ta APC kan kudurin kasafin kudin bana.

A Najeriya, har yanzu ana jani-in-ja-ka a kan kudirin kasafin kudin kasar na bana tsakanin 'yan majalisar wakilai 'yan jam'iyyar PDP da kuma takwarorinsu na jam'iyyar adawa ta APC.

Tuni dai jam'iyyar APC ta umurci 'ya'yanta da ke majalisar da su juya wa kasafin kudin baya har sai an tabbatar da doka da oda a jihar Rivers.

A halin da ake ciki dai majalisar ta mika kasafin kudin ga hannu wani kwamiti da zai yi nazari game da bukatar da bangaren 'yan jam'iyyar adawa ya gabatar cewa bai dace a yi muhawara a kan kudirin kasafin kudin ba bisa zargin cewa shugaban kasa ya saba wa wasu ka'idoji.

Yayin da ake ganin cewa wannan takaddama na kara girma, Hon Binta Bello, 'yar majalisar wakilai daga jihar Gombe, kuma 'yar jam'iyyar PDP, ta ce bai da ce a yi wasa da kasafin kudi ba, don haka suna kokarin shawo kan takwarorinsu.

Hon Binta Bello ta kara da cewa burin 'yan majalisa shi ne su tabbatar da zaman lafiya ci gaban kasa, ta kuma ce saboda matsalar Jihar River bai kamata ace za a dakatar da aiwatar da kasafin kudin ba alhalin akwai sauran jihohi a Najeriyar.

Karin bayani