'Kudancin Libya matattarar 'yan ta'adda ne'

Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

Gwamnatin Nijar ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan soja a yankin kudancin Libya, wanda ta ce ya zama wata matattara ta 'yan ta'adda, tun bayan da aka kawar da Kanar Gaddafi.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ne, Hasumi Mas'udu yayi wannan kiran, a lokacin ziyarar da ya kai a birnin Paris.

A cewarsa, kasashen yammacin duniya wadanda suka taimaka aka cire Gaddafi a yanzu ya kamata su sa hannu wajen magance abinda ya biyo bayan hakan.

Ministan ya ce masu leken asiri na Amurka sun yi gaskiya inda suka ce yankin Afrika kudu da hamadar sahara cibiyar masu tsatsauran ra'ayi ce.

Karin bayani