Ana zanga-zanga kan auren jinsi daya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana sa ran gudanar da zanga-zangar a birane da dama

Mutane da dama ne ke gudanar da zanga-zanga a kasashen duniya daban-daban domin kin jinin matakin da Rasha ta dauka na hana auren jinsi daya.

Wannan zanga-zanga na faruwa ne kwana guda kafin fara gasar a Olympics ta bazara a Sochi.

A birnin Melbourne na Australia, masu zanga-zanga sun yi kira ga manyan kamfanonin da ke daukar nauyin gudanar da gasar da su tsoma baki kan abin da jami'an gwamnati suka kira '' farfaganda game da auren jinsi daya''.

Ana sa ran za a gudanar da zanga-zanga a biranen New York da Paris da London.

Karin bayani