Yunkurin hana intanet a Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan adawa sun ce hakan yunkuri ne na hana mutane fadar albarkacin bakinsu

'Yan majalisar dokokin Turkiyya suna gudanar da muhawara kan kudurin dokar da zai bai wa gwamnati damar rufe shafukan intanet batare da karbo sammaci daga kotu ba.

Kudirin dokar zai tilastawa kamfanonin da ke samar da intanet su ajiye bayanan mutanen da ke amfani da shafukan na tsawon shekaru biyu, sannan su mika wa gwamnati idan ta bukaci hakan.

'Yan adawa sun yi tir da kudirin dokar, suna masu cewa yunkuri ne na dakile 'yancin fadar albarkacin baki.

Da ma dai gwamnati ta takaita yadda ake amfani da intanet a kasar.

Gwamnatin ta musanta zargin da ake yi cewa hakan yunkuri ne na hana mutane sukar ta.

Karin bayani