An kashe mutane 10 a Wase

Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption Gwamnan jihar Filato, Jonah Jang

Rahotanni daga jihar Filato a arewa ta tsakiyar Nijeriya, na cewa mutane fiye da goma ne suka rasu a wani tashin hankali da ya biyo bayan wani hari da wasu 'yan bindiga su ka kai a garin Wase da kuma kauyen Mavo.

Mazauna yankin dai na zargin 'yan kabilar Taroh ne da kai harin amma 'yan kabilar Taroh din kan musantan irin wannan zargi.

Mazauna karamar hukumar ta Wase sun bayyana cewa tun gabanin ketowar alfijir ne maharan dauke da bindigogi suka kai hari a garin Wase inda aka yi ta musayar wuta tsakanin jama'ar garin da kuma 'yan bindigar a bakin rafi na shiga garin kafin daga bisani maharani suka arce, amma mutum guda aka jikkata daga cikin jama'ar garin.

Kakakin rundunar 'yan-sandan jihar ta Filato DSP Fellicia Anslem ta bayyana cewa ba ta samu cikakken rahoton abin da ya faru ba saboda nisan wurin daga Jos baban birnin jihar.

Wasu mazauna yankin sun shaida mani cewa jami'an tsaro sun kai dauki domin tunkarar maharan wadanda aka fatattake su. Karamar hukumar Wase da ma sauran yankunan kudancin jihar ta Filato dai sun dade suna fama da rigingimu da kuma hare-hare masu nasaba da satar shanu da kuma batun kabilanci.

Karin bayani