Hukumar SSS ta sallami Asari Dokubo

Hakkin mallakar hoto ireporter
Image caption Asari Dokubo na goyon bayan Shugaba Jonathan

Hukumar tsaron farin kaya ta Nigeria watau SSS ta sallami shugaban kungiyar masu fafitikar 'yanta yankin Niger-Delta, wato Niger-Delta Volunteer Force, Mujahid Dokubo Asari wanda ta gayyata don amsa wasu tambayoyi.

Dokubo Asari ya yini a ofishin hukumar ta SSS dake Abuja a ranar Alhamis.

Wasu dai na ganin gayyatar da hukumar ta masa ba za ta rasa nasaba da wasu kalaman da ya dauki lokaci mai tsawo yana yi ba, cewa kungiyarsa za ta hana komai tafiya a Najeriya idan shugaba Goodluck Jonathan bai samu damar yin ta-zarce ba.

A baya dai an yi ta sukar hukumar SSS din da nuna wariya, lokacin da ta yi yunkurin tsare mataimakin sakataren jam'iyyar APC na kasa Mallam Nasiru El-Rufa'i sakamakon furucin da ya yi cewa za a fuskanci tashin hankali a Najeriya idan ba a yi adalci a babban zaben kasar da ke tafe badi ba.

Mujahid Asari-Dokubo ya kasance daya daga cikin masu goyon bayan Shugaba Jonathan ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara ta 2015.

Karin bayani