Gwamnatin Pakistan na tattaunawa da Taliban

Image caption Galibin 'yan Taliban suna zaune a kauyukan Pakistan ne.

Hukumomi a Pakistan sun ce an soma tattaunawa da wakilan 'yan kungiyar Taliban a karon farko don kawo karshen zubar jinin da ake yi na tsawon fiye da shekaru goma.

A yanzu haka dai wakilan gwamnati hudu da kuma wakilan Taliban uku na wata tattaunawa a wani ke bantaccen wuri don lalubo hanyar sulhu.

A farkon wannan makon aka shirya tattaunawa tsakanin bangarorin biyu amma sai wakilan gwamnati su ka ki bayyana saboda suna son 'yan Taliban su bada karin haske game da wakilansu da za a tattauna dasu.

Firaministan Pakistan, Nawaz Sharif ya ce yanason ya kawo zaman lafiya amma idan har 'yan Taliban suka ki yadda a tattauna watakila ya yi amfani da matakin soji.

Karin bayani