CFA 400bn: Tandja Mamadou ya bara

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tsohon Shugaba Tandja ya nemi a yi bincike kan kudaden da ya bari.

Tsohon shugaban Nijar, Malam Tandja Mamadou, ya yi kira ga hukumomin kasar da su gudanar da bincike a kan sojojin da suka hambarar da shi domin sanin abin da gwamnatinsa ta bari a baitulmalin kasar.

Tsohon shugaban kasar ya yi kiran ne a lokacin wani taron manema labarai a ranar Alhamis a birnin Yamai domin karin haske a game da kudaden nan, biliyan dari hudu na CFA da ya ce ya bari lokacin da sojoji, karkarshin jagorancin Janar Salou Djibo suka kifar da gwamnatinsa.

Tandja Mamadou ya ce kudaden da ya ce ya bari sun hada da biliyan dari uku na CFA da bankin raya kasashen Musulmai ta IDB ko BID ya ba Nijar a matsayin tallafi domin gina madatsar ruwan Kandadji, kuma kudaden na ajiye ne a Jeedah.

Haka zalika akwai kayyakin noma da takin zamani da kuma kayan abinci da aka ajiye a rumbun tsimin gwamnati, OPVN, wadanda darajarsu za ta kai kusan biliyan dari na CFA.

Batun kudaden da tsohon shugaban ya ce ya bari dai ya janyo cece-kuce a kasar ta Nijar, kuma a watan jiya ne gwamnatin kasar ta ce za ta gudanar da bincike a kan wannan al'ammari.

Wannan dai shi ne karon farko da Tandja Mamadou ya yi bayani ga manema labari tun bayan da aka hambarar da shi a shekara ta 2010.

Karin bayani