Bankin duniya zai kashe dala biliyan daya

Image caption Za a kashe kudin wajen daukar hotunan taswirar Afrika

Bankin Duniya zai kaddamar da wani aiki na dala biliyan daya domin daukar taswirar albarkatun kasa da Afrika take da su.

A cewar bankin aikin mai sunan taswirar dala biliyan zai fito da arzikin ma'adinan nahiyar da ba a tatsa ba ta hanyar amfani da hotunan tauraron dan Adam da kuma safiyon binciken albarkatun kasa.

Wani kwararre kan harkar hakar ma'adinai dake aiki da Bnkin duniyar ya ce akwai dibin albarkatun kasar da har yanzu ba a gano su ba.

Tuni dai bankin ya saka jari na dala fiye da miliyan 200 kan bunkasa bayanan hakar ma'adinai ga Afrika, sannan a halin yanzu yana da hannu a wani binciken neman ma'adinai ta sama a Malawi.