Dubban musulmai na gujewa daga CAR

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ganau sun ce an kona masallatai da gidaje da dama, sannan an sace kayayyakin da musulmai suka bari

Ganau a birnin Bangui na Jamhuriya Africa sun ce dubban musulmai ne ke gujewa rikicin addinin da ya ya barke tsakanin musulmai da kirista a kasar .

Sun shaida wa BBC cewa motocin a -kori-kura na daukar mutanen tare da rakiyar dakarun kasar Chadi.

Mutanen dai su ne rukuni na baya bayan nan da ke kokarin tsallakewa daga kasar don gudun rikicin.

Tuni dai dubban mutane suka tsallake zuwa kasashen Chadi da Kamaru.

Wakilin BBC ya ce an kori musulmai da dama daga Bangui da wasu yankunan kasar.

Kazalika an kona masallatai da gidaje, kuma an sace kayayyakin da mutane suka bari.

Karin bayani