Musulmi suna tserewa daga Bangui

Dubban musulmi sun tsere daga Bangui babban birnin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya bisa rakiyar dakarun Chadi.

Sune gungu na baya bayan nan da ya tsere wa tashin hankalin addinin dake ci gaba tsakanin Musulmi da Kirista masu rinjaye.

Dafifin Kiristoci sun yi layi kan hanyoyi suna shewa yayin da jerin motocin ke fita da musulmi daga birnin.

Wani gungun 'yan kallo ya kashe wani mutumin da ya faɗo daga wata motar sannan kuma suka sassare shi.

Peter Bouckaert, daraktan ayyukan gaggawa na kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights wanda yake a Bangui, ya ce ya ga ta'asar iri-iri.