India: Minista ya sauka saboda zargin lalata

Hakkin mallakar hoto BBC Urdu
Image caption Minisitan ya dauki matakin ne bayan an zarge shji da yunkurin yin lalata da wata likita.

Wani babban minista a yankin Kashmir na kasar India ya sauka daga mukaminsa.

Minisitan ya dauki matakin bayan an zarge shi da yunkurin yin lalata da wata likita.

Ana zargin Shabir Ahmed Khan, wanda shi ne ministan harkokin lafiya, da neman yin lalata da wata likitar mata lokacin da ya kira ta zuwa ofishinsa.

Wannan dai shi ne batun yunkurin lalata na baya bayan nan da ya shafi manyan jami'an gwamnatin kasar.

A farkon wannan shekarar, an zargi alkalai biyu da yunkurin yin lalata da mata.

Hana yin lalata da mata ya zama babban batun da ake son kawarwa a kasar tun bayan da aka yi wa wata yarinyar 'yar makaranta fyade a birnin Delhi a shekarar 2012, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta.

Karin bayani