Za a fara kwashe 'yan Syria

Wadanda rikicin Syria ya rutsa da su. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An bada damar kwashe fararen hula da tsofaffi da kananan yara da kuma mata daga garin na Homs.

Gwamnati da 'yan adawar Syria sun cimma yarjejeniyar kai kayan agaji garin Homs wanda aka yiwa kawanya har tsahon watanni goma sha takwas.

A yau juma'a ne za a fara kwashe mata da kananan yara da tsofaffi da kuma mutanen da suke son barin garin. Kamar yadda mataimakin ministan harkokin wajen Syria Faisal al-Mikdad ya shaidawa BBC, inda yace yarjejeniya da aka cimma tsakanin gwamnan Homs da babban jami'in MDD da ke Syria za ta fara aiki, kuma hakan zai ba fafaren hula da basu ji ba basu gani ba damar ficewa daga garin, tare da wadata wadanda ke son zama da kayan agajin da suke bukata.

Kimanin mutane dubu dari biyu da hamsin ne suka makale a birnin Homs, tare da daruruwan mayaka 'yan tawaye.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi marhabin da wannan batu ta na mai cewa wannan mataki ne na kawo karshen wahalar fararen hula a yakin da ake a kasar.

Karin bayani