Cece-Kuce kan taron Najeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnatin kasar ta bayyana yadda za a yi wajen zabo wakilan da za su halarci taron.

A Nijeriya, ana ci gaba da kace-nace kan babban taron duba makomar kasar wanda ake shirin gudanarwa, har ma gwamnati ta sanar da hanyoyin da za a bi don tsamo wakilan da za su halarci taron.

Furfesa Ango Abdullahi daya ne daga cikin dattawan Nijeriya daga arewacin kasar, wadanda tun farko suka nuna adawa da gudanar da babban taron na duba makomar kasa, kuma ya jaddada cewa har yanzu suna nan kan bakansu ba su sauya ra'ayi ba kan halartar taron.

Sannan kuma ba za su tura wakilai ba, duk kuwa cewa alamu sun nuna cewa gwamnatin Kasar gama shirinta tsaf dan gudanar da taron, don kuwa tuni aka fara soma batun nada mahalarta taron.

Farfesa Ango Abdullahi ya kara da cewa babu abinda za a kulla a taron bare ace za a bar arewa a baya, kuma shugaba Jonathan a watanni shida da suka gabata ya tsaya kai da fata kan cewa ba za a gudanar da taron ba.

Amma kwatsam a ranar 1 ga watan Oktobar shekarar da ta gabata wato ranar da Najeriya ta samu 'yan cin kai daga turawan mulkin mallaka, shugaba Jonathan ya sanar da cewa za a yi taron dan haka su sam ba su gamsu da batun taron ba.

Karin bayani