Sabuwar kungiya ce ta kai hari a Masar

Hakkin mallakar hoto Rueters
Image caption Tun bayan hambarar da Mohamed Morsi hare-hare kan jami'an tsaro suka zama ruwan dare a Masar

Wata kungiya ta 'yan jihadi da ba a santa ba a baya ta ce ita ta kaddamar da hare-haren bam har guda biyu wadanda suka raunata 'yan sanda shida ranar Juma'a a birnin Alkahira na kasar Masar.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar mai suna Ajnad Misr ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare, sannan ta yi kira ga jami'ai da sojojin kasar ta Masar su sauya sheka.

Ba a dai tabbatar da sahihancin sanarwar ba, wacce aka wallafa a shafin intanet da na Facebook na wata kungiya mai alaka da al-Qa'ida.

Munanan hare-haren bindigogi da na bama-bamai a kan jami'an tsaron kasar sun zama ruwan dare tun bayan da sojoji suka hambarar da Shugaba Mohamed Morsi mai kishin Islama a watan Yulin bara.

Karin bayani