Jonathan na ziyara a Sokoto

Shugaba Jonathan

A Yau ne shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara Jihar Sokoto a arewacin kasar inda ya karbi tsohon gwamnan jihar Attahiru Bafarawa wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta APC zuwa jam'iyyar PDP mai mulki.

Shugaban wanda yake tare da rakiyar jigajigan jam'iyyar da wasu gwamnonin jihohi na PDP ya sami tarba daga mataimakin gwamnan Sokoto Alhaji Mukhtar Shagari.

An dai tsaurara matakan tsaro a birnin na Sokoto dangane da zirarar shugaban kasar da yan tawagarsa.

Tsohon gwamnan jihar ta Sokoto Attahiru Bafarawa ya sauya sheka ne daga jam'iyyar adawa ta APC zuwa PDP bisa abin da ya kira rashin aldalci.

Karin bayani