Masu aikin umra 15 sun mutu a Madina

Saudiyya Hakkin mallakar hoto AFP

Musulmi akalla goma sha biyar ne dake gudanar da aikin umra suka rasu a birnin Madina na kasar Saudiyya bayan da gobara ta tashi a Otel din da suka sauka.

Wasu mutanen kimanin dari da talatin kuma sun sami raunuka galibinsu sakamakon shakar hayaki.

Jami'an agajin gaggawa sun kwashe baki kimanin dari bakwai da suka sauka a Hotel din.

A yanzu haka dai ana cigaba da gudanar da bincike domin gano musababbin aukuwar gobarar wadda ta yi ta ci har tsawon sa'oi biyu.

Karin bayani