'Yar Sarkin Spain ta gurfana a gaban kotu.

Gimbiya Cristina Hakkin mallakar hoto GETTY

Gimbiya Cristina, 'yar autar sarkin Spain Juan Carlos ta baiyana a gaban kotu a Mallorca game da zargin Almundahana.

Wannan dai shine karon farko a tarihin Spain da wata yar gidan sarautar kasar ta gurfana a kotu.

Ana tuhumarta ne game da wasu harkokin kasuwanci na mijinta Inaki Urdangarin wanda ake zargi da Almubanzaranci da miliyoyin daloli na baitulmalin kasa.

Dukkansu dai sun musanta aikata ba daidai ba.

Karin bayani