An kai hari akan tawagar agaji a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP

An kai hari akan tawagar Majalisar Dinkin Duniya yayin da ta ke kan hanya domin raba kayan agaji ga jama'a a birnin Homs dake karkashin ikon 'yan tawaye.

Kafar yada labaran gwamnati ta ruwaito cewa ma'aikatan agaji hudu na kungiyar Red Crescent sun sami raunuka.

Kungiyar ta zargi yan tawaye a birnin Homs da kai harin.

A waje guda dai 'yan tawayen sun zargi sojojin gwamnati da cigaba da yin luguden wuta a birnin Homs tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki ukku a ranar Juma'a.

Karin bayani