Za a fara tattaunawar sulhu kan Syria

Tattaunawar sulhu kan kasar Syria a Geneva Hakkin mallakar hoto c
Image caption Tattaunawar sulhu kan kasar Syria a Geneva

Bangarori biyu dake tafka yakin basasa a Syria za su fara tattaunawar zaman lafiya a karo na biyu a birnin Geneva ranar Litinin.

Tattaunawar farkon ta gamu da cikas a makon jiya bayan da aka tashi baram-baram ba tare da wata nasara ba game da batun kawo karshen fadan.

Sai dai lugudan wutar da ake yi ya karya yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin kuma babu tabbacin ko hakan zai kai ga sauran wasu wuraren.

Kungiyar agaji ta Red Cresent dake Syria ta ce mata da yara da gajiyayyu fiye da 600 ne aka kwashe daga birnin Homs mai fama da tashin hankali.

Sai dai akwai karar lugudan wuta da musayar harbe-harbe da ake cigaba da yi a lokacinda mutanen ke shiga motocin safa-safa za su fice daga cikin birnin.