PDP ta sace kayan rajista a Gombe - APC

Zabe a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zabe a Najeriya

Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta zargi matasan jam'iyyar PDP a jihar Gombe da sace kayan rajistarta, yayin da ta ke rajistar 'yayanta a fadin kasar.

Shugaban riko na jam'iyyar APC a karamar hukumar Balanga, Mr Bwilimri Jacob, ya ce matasa kimanin 30 sun kai farmaki a ofishinsu dake yankin Cham su ka kuma arce da takardun rajistar.

To sai dai kuma a cewar shuwagabannin jam'iyyar PDP mai mulki, babu hannun jam'iyyar a harin.

Ko a cikin makon ma dai wasu matasa da jam'iyyar APC ke zargin cewa yan jam'iyyar PDP ne sun kona ofisoshi da wasu kadarori na jam'iyar adawar ta APC a karamar hukumar Nafada dake cikin jihar Gomben kodayake 'yan PDP na nesata kansu da barnar.

Rundunar 'yansandan jihar ta Gombe ta ce tana gudanar da bincike.

Karin bayani