'Yan bindiga sun kai hari a Filato

Rahotanni daga karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filaton Nijeriya na cewa wasu yan bindiga sun kai hari kan makiyaya.

Maharan sun kashe biyu daga cikin makiyayan sannan suka yi awon gaba da shanu fiye da dari daya.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Gero dake kusa da garin Bukur hedikwatar karamar hukumar.

Jihar Filato dai ta dade tana fama da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabinlanci da addini da kuma siyasa inda lamarin a baya-bayan nan ya fi Kamari kan batun satar shanu da kuma kai hare-hare a kauyuka.