Switzerland ta amince da takaita shigar baki

Hakkin mallakar hoto AP

Jama'ar Switzerland sun kada kuri'a da karamin rinjaye a zaben raba gardamar da aka gudanar domin tilasta iyakance adadin baki yan kasashen waje da za su shiga cikin kasar domin zama ko aiki.

Hakan dai ya kawo karshen yarjejeniyar da ta Switzerland din ta rattaba hannu da kungiyar tarayyar turai na bada izinin shige da ficen baki ba tare da shamaki ba a tsakanin al'umomin kasashen kungiyar tarayyar turai.

Yan kasar sun amince da shawarar da kankanin rinjaye na kashi hamsin da digo biyar cikin dari na yawan kuri'un da aka kada. Pierre Schifferli shine mai magan da yawun jam'iyyar Swiss peoples party wadda ta gabatar da shawarar kuri'ar raba gardamar.

Karin bayani