Ana kidayar kuri'ar raba gardama a Switzerland

Hakkin mallakar hoto AP

Ana kidayar kuri'ar raba gardama a Switzerland kan ko kasar ta kawo karshen yarjejeniyar da ta kulla da tarayyar turai kan shigar da kayayyaki kasashen juna ba tare da shamaki ba, da kuma tsaurara matakan bawa ma'aikata 'yan kasar waje damar ayyuka a kasar.

Jam'iyyar Swiss People ita ce ta gabatar da bukatar yin kuri'ar raba gardamar, bayan tace yawan shigowar bakin haure na yin illa ga tattalin arziki da kuma ingancin rayuwar al'umar kasar.

Gwamnatin kasar da shugabannin 'yan kasuwa sun ce kawar da shamaki a shige da ficen ma'aikata tsakanin bangrorin biyu na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasar.

Kasar Switzerland dai ba mamba ce a kungiyar tarayyar turai ba amma ta amince da shige da ficen kayayya ba tare da shamaki ba dan ta kasance cikin kasuwar bai daya.

Karin bayani