Gwamnatin Birtaniya ta soke jarrabawar ETS

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firaministan Birtaniya, David Cameron

Gwamnatin Birtaniya ta soke wata fitacciyar jarrabawar harshen Turanci bayan BBC ta bankado cogen da ake yi da ita wajen bada Visa ga dalibai da ke son zuwa kasar karatu.

Cikin sirri masu bincike na BBC sun dauki hotunan bidiyo lokuttan da ake aikata satar amsa da kuma cuwa-cuwa iri-iri yayin jarrabawar da gwamnati ta amince da ita, kuma wacce sai mutum ya ci jarrabawar kafin ya samu Visa zuwa karatu nan Birtaniya.

Kamfanin da yake gudanar da jarrabawar wato ETS ya ce, yana iyakar kokarinsa wajen ganowa da kuma hana aikata duk wata cuwa-cuwa yayin jarrabawar.

Karin bayani