Ambaliyar ruwa ta kashe mutane a Burundi

Image caption Ambaliyar ta rutsa da mutane da dama

Mutane da dama ne suka mutu, wasu dama kuma sun jikkata sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da kuma zabtarewar kasa a Bujumbura, babban birnin Burundi.

Wasu rahotanni dai na cewa, mutanen da suka mutu sun kai hamsin.

Wani mutum ya ce, danginsa tara sun mutu sakamakon ambaliyar ruwan.

Sai dai kuma wakilin BBC a birnin Bujumbura ya ce, zai yi wuya yanzu a tantance yawan wadanda suka mutu saboda akwai gawarwakin da laka ta lullube.

Yanzu haka dai wurin ajiyar gawa na babban asibitin birnin ya cika makil.

Karin bayani