CAR: Wasu musulmai sun ce ba za su gudu ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shagon wani musulmi da aka lalata

Wasu daga cikin al'ummar musulmi dake Jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun ce ba za su bar kasar ba, duk da barazanar da suke fuskanta daga mayakan kiristocin kasar.

Duk da cewa dimbin Musulmi sun bar kasar, har yanzu akwai kamar dubu takwas a babban birnin kasar Bangui.

A kusan kullum sai an sami rahotannin kashe-kashe a kasar.

Wani bahaushe Alhaji Hadi Kabara Wananga ya shaidawa BBC cewar ba za su bar kasar ba, sai dai a kashe su.

Ko a karshen mako ma sai da aka kashe wani dan Majalisar dokokin kasar, wanda ya soki lamarin hare-haren da ake kaiwa musulmi.

Karin bayani