Da na zama almajiri -Jonathan

Image caption Jonathan ya ce shi dan talakawa ne, don haka da a Sokoto yake da ya zama almajiri

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ce da a jihar Sokoto aka haife shi, to da ya zama almajiri.

Mista Jonathan ya kara da cewa kasancewarsa dan talakawa, da a Sokoto ya girma da ya zama almajiri --- ganin cewa akasarin almajirai talakawa ne.

Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara Sokoto a karshen makon jiya.

Sai dai jam'iyyar APC mai mulkin jihar ta ce bai cancanta shugaba kamar Jonathan ya rika yin irin wadannan kalamai ba.

Ta ce Mista Jonathan ya mayar da 'yan jihar kamar almajirai.

Karin bayani