Switzerland za ta rage shigar baki

An kada kuri'ar da aka kada a Switzerland Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Takaita shigar baki daga Turai a Switzerland

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta sake nazarin dangantakarta da Switzerland bayan wata kuri'ar raba gardama da aka kada a kasar ta nemi a tsaurara matakan shigar baki 'yan kasashen Turai.

Kuri'ar da aka kada da dan karamin rinjaye ta nuna mazauna yankunan karkara suna goyon bayan a sake farfado da matakai masu tsauri na shigar baki kasar, a yayinda mazauna birni suka nuna rashin amincewarsu.

Wannan shawara dai za ta iya yin barazana ga yarjejeniyoyi da dama da kasar ta kulla da Tarayyar Turai, abinda ya hada da kafar shiga kasuwar Tarayyar Turan, inda kasar ke sayar da fiye da rabin kayan da take fitarwa zuwa kasashen waje.

Ministan harkokin waje na Switzerland Didier Burkalter ya ce, ya yi shirin kai ziyara manyan birane na kasashen Turan kuma zai fara da birnin Berlin domin yin bayani game da kuri'ar da aka kada tare da neman hanyar da za a warware matsalar.

Karin bayani