Jirgin saman sojin Algeria ya yi hadari

Image caption Dakarun tsaron Algeria

Rahotanni da Algeria na cewar wani jirgin saman soji ya fadi dauke da mutane fiye da dari daya a cikinsa.

Gidan talabijin na kasar ya ce jirgin ya fadi ne a lardin Oum El Bouaghi mai cike da tsaunuka dake kudu maso gabashin Algiers babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce jirgin na dauke da iyalan wasu sojoji ne.

Kawo yanzu dakarun kasar basu fitar da wata sanarwa ba game da batun.

An tura masu agajin gaggawa don taimakawa wadanda suka tsira sakamakon hadarin jirgin.