Mutane 34 aka kashe a harin Konduga

Jami'an tsaro a jihar Bornon Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro a jihar Bornon Najeriya

Gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar da kashe mutane34 sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai a garin Konduga na jihar.

Maharan da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun jikkata mutane da dama, tare da kona gidaje masu yawa a garin.

Gwamnan jihar Bornon, Alhaji Kashim Shettima, ya ziyarci garin Kondugan don yin ta'aziyya ga al'ummar garin inda ya yi alkawarin tallafa musu.

Kakakin Gwamnan Jihar, Isa Umar Gusau, ya ce gwamnatin na shirin tura kayan taimako da na gyaran gidajen da aka kona ga jama'ar garin na Konduga.

Tun farko dai wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa an kashe akalla mutane 40 a unguwa daya kadai.

Kawo yanzu dai ma'aikatan agaji sun kwashe wadanda aka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri.

Wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross da ke Konduga, Comrade Bukar Mai Rembe ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun bude wuta ne a bangarori daban-daban na garin ciki har da kasuwanni.