"Tattalin arzikin Kamaru zai bunkasa"

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Kamaru Paul Biya

Shugaban kasa Paul Biya ya ce tattalin arzikin Kamaru zai iya bunkasa da kashi 5% daga bana.

Ya bayyana hakan ne a wani jawabin da ya saba yi wa matasa a jajiberen bikin ranar da aka ware musu ta 11 ga Fabrairun ko wace shekara.

Hakan kuma in ji shugaban na iyahaifar da aikin yi sama da 25,000.

Manufar gwamnatin Kamarun ita ce samun damar jerawa kafada da kafada da kasashen da su ka ci gaba irin su Mexico da Malaysia nan da shekaru 20.