Hijirar 'yan kasuwa na kara yunwa a CAR

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubunnan Musulmi na tserewa daga CAR

Kungiyoyin agaji na duniya na gargadin cewa karyewar kasuwanci a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zai kara ta'azzara karancin abincin da ake fama da shi.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyata cewa kaso 90% na al'ummar kasar na cin abinci ne sau daya a yini, amma ficewar da 'yan kasuwa ke yi daga kasar za ta iya tabarbara al'amarin.

Hare-haren fansa tsakanin Musulmi da Kirista sun hallaka mutane da dama tare da tilasata wa dubunnan Musulmi tserewa zuwa Chad mai makwabtaka.

Binciken da kungiyoyin Oxfam da Action Against Hunger su ka gudanar ya nuna dillalan hatsin da su ka rage a Bangui babban birnin kasar ba su kai 10 ba, abin da ke haddasa karancin abinci da hauhawar farashi.

Tuni dai nama ya yanke a birnin bayan da makiyaya suka tsere da dabbobinsu zuwa dazuzzuka.

Haka kuma kaso 96% na manoman kasar ba su da irin shuka, wata guda kafin faduwar damuna.

Rikicin kuma ya hana a shigar da abinci daga kasashen waje, inda a yanzu haka daruruwan motocin dakon abinci ke tsaye kan iyakar kasar da Kamaru saboda direbobinsu na gudun farmaki daga 'yan bindiga.

Karin bayani