Ministan tsaron Faransa zai ziyarci CAR

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana ci gaba da rikicin addini a CAR

Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian zai ziyarci Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ranar Laraba a ci gaba da kokarin kawo karshen rikicin kasar.

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya bukaci Faransa ta kara yawan sojojinta a jamhuriyar domin hana raba kasar zuwa bangarorin Kirista da Musulmi.

Dakarun Faransa 1,600 ne dai su ke aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Faransan ta bukaci majalisar dinkin duniya da ta tura rundunar kiyaye zaman lafiya ba tare da bayyana ko za ta kara adadin na ta dakarun ba.

Karin bayani