MUJAO ta sace 'yan Red Cross a Mali

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakatun MUJAO a Gao.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP ya ce masu kishin Islama ne su ka sace tawagar ma'aikatan agaji na Red Cross da ta bace a arewacin Mali.

AFP ya ce wani wakilin kungiyar masu fafutukar Islakma ta MUJAO ya tabbatar da cewa sun kama wata mota dauke da jami'an Red Cross a cikinta.

Hukumar Red Cross ta duniya ta ce wata motarta ta bace ranar Asabar a tsakanin garuruwan Kidal da Gao.

Ma'aikatan Red Cross hudu ne a cikin motar tare da wani ma'aikacin wata kungiyar agajin ta dabam.

Karin bayani