'Yan majalisar wakilai 5 sun koma PDP

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Hakan dai ya sa yanzu PDP na da 'yan majalisa 178 members, yayin da APC ke da 168 a majalisar ta wakilai.

'Yan majalisar wakilai biyar na jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria.

Kakakin majalisar, Aminu Tambuwal, ne ya bayyana sunayen 'yan majalisar lokacin zaman majalisar na ranar Talata.

'Yan majalisar da suka koma PDP su ne Ladan Shehu Bichi (Kano), Abdulsalam Adamu (Kano), Sani Umar Dangaladima (Zamfara), Shehu Gusau (Zamfara) da Umar Bature (Sokoto).

Kazalika dan majalisar, Isa Mohammed Bashiru, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Hakan dai ya sa yanzu PDP na da 'yan majalisa 178 members, yayin da APC ke da 168 a majalisar ta wakilai.

Karin bayani