Syria: Akwai sarƙaƙiya a kan aikin agaji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lakhdar Brahimi, jagoran sulhunta rikicin Syria

Wakilan majalisar ɗinkin duniya suna ci gaba da tattaunawa da ɓangarorin gwamnatin Syria da 'yan tawaye domin tabbatar da cewa, masu kai kayan agaji birnin Homs ba su fuskanci wata barazana ba.

Ƙungiyoyin agaji a Syria sun dakatar da aikin kwashe mazauna birnin Homs da yaki ya rutsa da su, yayin da kuma alamu ke nuna cewa, babu wani cigaba da ake samu a taron zaman lafiyar da ake yi.

Dangane da tafiyar hawainiya da tattaunawar zaman lafiyar ke yi, mai shiga tsakani a rikicin na Syria amadadin majalisar dikin duniya, Lakhdar Brahimi cewa yayi, lamarin haka yake.