APC ta zargi PDP da baiwa 'yan majalisa kudi

Image caption Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Bisi Akande

Jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta zargi jam'iyyar PDP mai mulkin kasar da baiwa 'yan majalisar dokoki makudan kudade don su kara komawa PDP.

Kakakin APC, Lai Mohammed a wata sanarwar ya zargi PDP da yin amfani da kudin al'umma inda ta kwadaitar da duk wani sanata da ya yarda ya koma PDP za ta bashi dalar Amurka miliyan biyu sannan kuma duk dan majalisar wakilai da ya amsa goron gayyatar za ta bashi dala miliyan daya.

A cewar APC din kuma duk wani kusa a jam'iyyarta da ya amince ya koma PDP za a bashi dala miliyan goma.

Jam'iyyar APC din wacce ta yi Allahwadai da lamarin, ta kuma yi zargin cewar an kwadaitar da 'yan majalisar wakilai daga jihar Rivers toshin dala miliyan biyar idan suka watsar da APC suka koma PDP.

A cewar APC din wannan abu ba zai hana al'umma kawar da PDP ba a zaben 2015.

Ana saran nan gaba jam'iyyar PDP za ta maida martani.

A ranar Talata ne PDP din ta kara samun rinjaye a majalisar wakilan Nigeria bayan da wasu 'yan majalisa biyar suka bar APC suka koma PDP.

Karin bayani