Jonathan ya sallami ministoci hudu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnatin Jonathan ba ta bayyana dalilin cire ministocin ba

Rahotannin daga Nigeria sunce shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya sallami wasu ministoci akalla 4 daga cikin gwamnatinsa.

Ministocin da aka sallama daga bakin aikinsu sun hada da Madam Stella Oduah, ministan sufurin jiragen sama, wadda a kwanakin baya aka zarga da sayen wasu motocin sulke guda biyu a kan kudade sama da Naira miliyan dari biyu.

Akwai kuma Godswin Orubebe na ma'aikatar dake kula da Niger Delta, da Caleb Olubolade (Harkokin 'Yan sanda) da kuma Yerima Ngama (Kudi).

A cikin watan Satumba ne, Shugaba Jonathan ya sallami ministoci tara.

Ministocin sune:Ruqayatu Rufa'i (Ilimi); Zainab Kunchi (Makamashi); Bukar Tijjani (Aikin gona), Shamsudeen Usman (Tsare-tsaren kasa) da Olusola Obada (Tsaro).

Sauran sune: Ita Okon (Kimiya da Fasaha); Olugbenga Ashiru (Harkokin kasashen waje); Ama Pepple (Kasa da sifiyo) da kuma Hadiza Mailafia (Muhalli).

Kawo yanzu fadar shugaban kasa ba ta baiyana dalilin sauke su ba.

A Larabar nan dai majalisar dattawan Nigeria ta fara tantance mutanen da shugaba Jonathan ke neman nada wa sababbin ministoci.

Karin bayani