Ba cin zarafin wadanda aka kama a Homs

Birnin Homs
Image caption Mutanen dake ficewa daga birnin Homs

Gwamnan birnin Homs a kasar Syria Talal al-Barazi ya sake ba da tabbacin cewa cikin mutanen dake barin birnin, ba a cin zarafin maza da za su iya shiga fagen-daaga.

Fiye da maza 350 ne aka tura zuwa cibiyar bincike kuma gwamnan ya gaya wa BBC cewar za a gurfanar da 34 daga cikinsu gaban kotu inda za a caje su da laifukka ko dai na agaza wa 'yan tawaye a fadan da suke yi da gwamnati, ko kisan kai, ko kuma guje wa shiga aikin soji.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana sa ido a kan mutanen da aka rike.

A lokacin da wa'adin tsagaita wutar da aka kulla ke karewa ranar Laraba, za a cigaba da kokarin kara fitar da wasu farar hular daga Homs da kuma kai kayan agaji ga mutanen da har yanzu aka yi wa kofar-raggon.

Daya daga manyan Shugabannin kungiyar adawa ta Syrian National Coalition, Monzer Akbar ya ce ya na cikin damuwa game da abin da zai samu mutanen da a yanzu ke hannun gwamnatin.

Karin bayani