An sako fursinoni 65 a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Makwancin fursinoni a kurkukun Bagram

Shugaba Karzai na Afghanistan ya bada umurnin sakin fursinoni 65 wadanda yawanci suna da alaka da kashe dakarun kasar da kuma sojojin kasashen wajen masu kokarin kawo zaman lafiya.

Amurka ta ce tana da kwararan hujjoji a kan cewar wadanda aka tsare din, na da hannu a tada bam da kuma wasu hare-haren.

Shugaba Karzai ya ce yawancin fursinonin basu da laifi.

A cewarsa galibin fursinonin yara ne da tsofaffi wadanda aka tsare a kurkuku na Bagram inda ake azabtar dasu kuma ana saka musu kiyayya a kan kasarsu.

Ofishin jakadancin Amurka a Kabul ya bayyana matakin sakin fursinoni a matsayin abun takaici.

Masu aiko da labarai sun ce wannan matakin zai gurgunta dangantakar dake tsakanin Amurka da Aghanistan.

Karin bayani