Liverpool ta sha da kyar a Fulham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Steven Gerrard ya kwato Liverpool da fenariti.

Steven Gerrrard ne ya buga fenaritin da ta ceto Liverpool tare da ba ta tazarar maki hudu tsakaninta da jagorar Premier bayan da ta tsira da kyar a Fulham.

Cin gidan da Kolo Toure ya yi ce ta sa Fulham a gaba kafin Daniel Sturridge ya farke.

Kieran Richardson na Fulham ya kara guda sannan Philippe Coutinho na Liverpool ya kara farkewa.

Fenaritin ta Gerrard dai ta bai wa Liverpool damar ci gaba da sa ran daukar kofin Premier a bana.