Ana takaddama kan nada Ministocin Nigeria

Majalisar Dattawan Nijeriya Hakkin mallakar hoto peoples daily
Image caption Majalisar Dattawan Nijeriya

Majalisar dattawan Nigeria za ta ci gaba da tantance sunayen da shugaban kasar ya aika musu, wanda yake son nada musu mukamin minista.

Kawo yanzu dai majalisar ta tantance mutune shida cikin 11 da ya mika musu.

To, sai dai an samu sabanin ra'ayi tsakanin wasu 'yan majalisar lokacin tantance tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro, wato Janar Aliyu Gusau mai ritaya.

Hakan ya biyo bayan kyale shi da shugaban majalisar dattawan Senata David Mark ya yi, ya yi tafiyarsa ba tare da ya amsa tambayoyi ba.

Karin bayani