"Ba na nadamar wasikata ga Jonathan"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Obasanjo ya dakatar da ayyukansa a PDP

Tsohon Shugaban Nigeria, Cif Olusegun Obasanjo ya ce ba ya nadama kan wasikar da ya rubutawa Shugaba Jonathan inda ya caccakeshi game da salon mulkinsa.

A cikin wata hira ta BBC an tambaye shi ko mecece manufarsa ta rubuta wasika ga Najeriya mai ci, Goodluck Jonathan a watan Disamban bara?

Obasanjo yace "Wasikar ai ba ta fito-na-fito ba ce, wasika ce a kan batutuwan da suka shafi kasa, kuma idan shugaban kasar yana so ya tattauna da ni a kan dangantakata da shi ko wani batu da ya kebanta garemu, kofata a bude ta ke. Tun bayan rubuta wasikar mun yi magana kusan sau shida".

Ya kara da cewar baiyi nadamar rubutawa Jonathan wasika ba "Don me zan yi nadama? Kana yin nadama ne idan ka gaza yin abin da ya kamata ka yi kuma ba ka da sauran lokacin yinsa. Abin da ya kamata mutum ya yi nadamrsa ke nan a rayuwarsa. Amma wasikar da ta zo a kan gaba, wacce ya kamata ka rubuta, kuma ka rubuta, bai kamta ka yi nadamar rubuta ta ba".

Tun bayan saukarsa daga kujerar mulki, Cif Obasanjo na shiga ana damawa da shi a al'amura da dama a fadin nahiyar Afirka, ga shi kuma manoma.

Haka zalika ya kan yi amfani da matsayinsa na dattijo don kara fitowa fili da wasu abubuwa da suka addabi al'umma; a baya-bayan nan ma ya kirkiri Gidauniyar Obasanjo, wacce ke duba batutuwan da suka shafi matasa.

Karin bayani